✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfara ta tura malamai 97 Umrah su roka mata nasara kan ‘yan ta’adda

Malaman za su ba da himma wajen yi wa jihar da ma Najeriya addu’o’i a wuraren da ake amsar addu’o’ia Makka da Madina.

A wani mataki na kawo karshen ’yan fashin daji a Zamfara, gwamnatin jihar ta tura malamai 97 zuwa Umrah domin su roka wa jihar tsari daga sharrin ’yan ta’addar.

A ranar Laraba malaman suka tashi zuwa Kasa Mai Tsarki inda ake sa ran su ba da himma wajen yi wa jihar da ma Najeriya addu’o’i a wuraren da ake kyautata zaton amsar addu’o’in bayi a Makka da Madina.

Sa’ilin da yake yi wa malaman jawabi gab da tashin nasu, mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, ya bukace su da su sanya Jihar Zamfara da al’umarta cikin addu’o’insu da zummar ganin bayan matsalolin da suka addabi jihar da ma kasa baki daya.

A nasa bangaren, Malam Atiku Balarabe, ya yi wa malaman huduba kan yadda ya fi dacewa su gudanar da ibadojinsu yayin zaman nasu a Saudiyya.

Malamin ya ja hankalin takwarorin nasa kan su yawaita tuna cewa an tura su Umurah ne don su wakilci al’umar Zamfara da kuma neman taimakon Allah wajen kawo karshen harkokin ta’addanci a fadin jihar.

Idan dai za a iya tunawa, a farkon wannan watan ne Gwamnatin Zamfara ta raba wa sarakunan jihar motoci na alfarma sama da 200.