✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfara: ’Yan bindiga sun yi wa mutane luguden wuta a kasuwa

Sun je kasuwar neman a sako 'shanunsu da aka sace'.

’Yan bindiga sun kai farmaki Kasuwar ’Yar Tasha da ke yankin Dansadau, Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara inda suka kashe mutum daya suka kuma jikkata wasu da dama.

’Yan bindiga daga kusurwa ne suka far wa kasuwar a kan babura daga suna luguden wuta babu kakkautawa sannan suka yi awon gaba da kayan jama’a.

Kasuwar ’Yar Tasha da ke ci a ranakun Alhamis ta shahara wurin sayar da dabbobi da hatsi, kuma ta sha fama da irin wadannan hare-hare.

Wani mazaunin garin mai nisan kilomita 25 daga Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ya ce maharan sun kai farmakin ne da Azahar inda suka yi da harbin duk wanda suka gani a kasuwar.

 

Abin da ya kawo harin —Mazauna

An kai wa kasuwar harin ne bayan wasu ’yan bindiga sun shigo kasuwar suka nemi sayar da dabbobi su saki wasu shanu da ’yan bindigar ke ikirarin cewa nasu ne da aka sace.

“Sun shiga bangaren masu sayar da dabbobi, suka nuna wasu shanu cewa a sake su domin nasu ne aka sace.

“Nan take sai dillalan suka shiga tattauna yadda za su saki shanun saboda sun san abin da zai iya biyowa.

“Ana cikin haka, sai wasu ’yan bindigar suka kira ’yan uwansu da ke cikin daji a waya, ba a jima ba suka shigo kasuwar suka fara harbin jama’a,” inji wani dillalin shanu.

 

Gudun famfalaki

Wani mazaunin garin ya ce, “Kasuwar da unguwannin kusa da ita an shi dimuwa, ’yan kasuwa na ta gudun tsira da ransu, wasunsu sun samu munanan raunuka.

“Ina zaune a kofar gida sai na fara jin karar harbi, kafin ka ce kwabo kowa ta kansa ya ke yi, nan na samu na rarrafa na shige gida na kulle.

“Daga cikin gida ina hango hayakin da ke tashi na runfunan da suka kona.

“Ina ganin yawancin mutanen da suka tsere suka bar kayan da suka kasa ba za su dawo ba, sai ’yan kadan masu jarumta.

“Amma yanzu ina jin maharan sun tafi, saboda an kira ni a waya an shaida min cewa an tsinci gawar mutum daya.

“Amma fa ’yan bindigar sun yi awon gaba da kayan da aka tafi aka bari musamman dabbobi da tufafi; Gaskiya mun ga tashin hankali.”

 

Jami’an tsaro sun kai dauki

Ya ce Allah Ya taimaka jami’an ’yan sanda da ke kusa da yankin da kasuwar take sun yi saurin kawo dauki, shi ya sa abin ya zo da sauki.

A cewarsa, maharan sun janye ne bayan zuwan ’yan sanda a cikin motar yaki.

Ya ce daga nan sai maharan suka janye, amma suna harbin ’yan sanda, su kuma nan take suka mayar da martani.