✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfara: Zan yi murabus idan za a samu zaman lafiya —Matawalle

Abin da ni da sauran 'yan Najeriya ke so shi ne ganin an kawar da mugayen irin.

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya ce a shirye yake ya ajiye mukaminsa idan har hakan zai kai zamar da zaman lafiya da tsaro a Jihar.

Matawalle ya ce hana shawagin jirage da hakar maadinai a jihar ta yi a Zamfara “ya yi daidai kwarai, saboda abin da ni da sauran yan Najeriya ke so shi ne ganin an kawar da mugayen irin daga kasar nan.”

Sai dai “ya kamata Majalisar Tsaron Kasa ta gayyace ni in ba ta wasu muhimman bayanai da za su taimaka wajen tunkarar matsalar da magance ta,” amma ya ce duk da haka matakin ya yi daidai.

“A shirye nake kuma na amince da duk wata mafita muddin za ta kai ga samuwar zaman lafiya a jihata,” inji shi.

Ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels kan sace dalibai mata 279 da yan bindiga suka sako bayan sun yi garkuwa da su daga makarantar GGSS Jangebe.

Ya ce, “Idan yin murabus di na daga kujerar Gwamna zai sa mutane su kwana da idanunsu biyu, zan sauka, ba ni da yunwar mulki, ina kwana ido biyu don kare Zamfarawa.”

Da yake karin bayani kan daliban da aka sako, Matawalle ya ce, ba a biya ko sisi na kudin fansa ba.

“Babu abin da aka biya don fansar yaran; mun yi amfani ne da tubabbun su (‘yan bindiga).

“Su ke tattauna da su kuma na ce ya kamata su tambaye su dalilin da ya sa suka aikata hakan ”.