✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan amince da nasarar Binani muddin ta kada ni a mazabarta —Ardo

An daina yaudarar jama'ar Jihar Adamawa da dan wani na goro da za a basu su kada kuri'a.

Dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa a jam’iyyar SDP, Dokta Umar Ardo, ya yi alkawarin saduda da zaben jihar muddin takwararsa ta jam’iyyar APC, Aisha Dahiru Binani ta yi nasara a Karamar Hukumar  Adamawa ta Kudu da ke zaman mahaifarta.

Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Talata, Ardo ya ce ba za a sake yaudarar al’ummar jihar da dan wani na goro da za a basu ba, sai dai su duba cancanta yayin kada kuri’arsu.

“Na fadi haka a baya a gidan Talabijin na kasa, kuma ina sake maimaitawa a yanzu ma.

“Idan har Binani ta yi nasara a mahaifarta [Karamar Hukumar Adamawa ta Kudu], to tun a nan zan amince da sakamakon, na bari a rantsar da ita a matsayin Gwamnar jihar”, a cewarsa.