✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan ba wa masu tada tarzoma a Najeriya mamaki —Buhari

Buhari ya ce masu tada tarzoma za su fuskanci tsattsauran hukunci.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya yi alkawarin ba wa wadanda suke kitsa tarzoma da tashin-tashina a fadin Najeriya mamaki.

Shugaban na wadannan kalaman ne yayin ganawarsa da Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kan jerin hare-haren da ake kai wa ofisoshinta a yankin Kudu-maso-Gabas da kuma Kudu-maso-Kudu.

  1. Rochas ya bukaci a zurfafa bincike kan kisan Gulak
  2. Matsalar tsaro: Buhari ya gana da shugabannin INEC

Buhari ya ce, “Kullum ina samun rahoton hare-hare da ake kai wa, hakan kuma ya nuna duk masu hannu a ciki ba sa so wannan gwamnati ta yi nasara.

“Matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta ta zama abun fada a fadin duniya. Masu yunkurin ruguza wannan gwamnati za su sha mamaki nan ba da jimawa ba. Mun ba su isasshen lokaci,” a cewar Shugaba Buhari.

Shugaban ya bayyana yadda ya zagaya jihohi 36 da ke fadin Najeriya, a lokacin yakin zaben 2019 kuma mutane suka amince masa.

Sannan ya yi alkawarin ci gaba da jan ragamar kasar bisa tafarkin Kundin Tsarin Mulki ya tanadar.

Buhari ya gargadi wadanda suke kitsa tarzoma da ta’addanci don dakile nasarar gwamnatinsa da su jira hukunci da zai biyo baya nan ba da jimawa ba.

Har wa yau, a cikin martanin nasa, ya ce masu tayar da tarzoma a wasu yankunan kasar matasa ne, ba su da masaniyar rayukan da aka rasa a lokacin yaki basasa.

“Wasu daga cikinmu da suka shafe watanni 30, a lokacin yakin, ya kamata su fadakar da su a harshen da za su fahimta. Saboda nan da wani lokaci za mu dauki tsattsauran mataki.”

Shugaban Kasa, a cikin wani jawabi da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya ce Hafsoshin Tsaro da Sufeto Janar na ’Yan Sanda za su dauki ragamar kawo karshen hare-haren.

Kazalika, da ya ke magana kan hare-haren bata-gari kan ofisoshin INEC, Buhari, ya ce gwamnatinsa za ta bai wa hukumar dukkan gudunmawar da ta ke bukata don tabbatar da gudanar da babban zabe da yake tunkarowa.

Da yake nasa jawabin, Shugaban INEC, Farfesa Yakubu, ya ce kwao yanzu Hukumar na da rahoton farmaki 42 da aka kai kan ofisoshinta tun bayan kammala babban zaben da ya gabata.