✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan bar Juventus a karshen kaka — Buffon

Ana yi wa Buffon kallon daya daga cikin masu tsaron ragar da suka yi fice a duniya.

Gianlugi Buffon, mai tsaron ragar Kungiyar Juventus da ke buga gasar Serie A a Italiya, ya ce lokaci ya yi da ya kamata ya rabar kungiyar, inda ya ce zai yi bankwana da ita yayin da kwataraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana.

Sai dai Buffon wanda ya lashe kofin duniya a 2006, ya ce dayan biyu ne, ko ya hakura da murza leda, ko kuma ya koma wata kungiyar idan har ya samu tayin da ya kwanta masa a rai kamar yadda shafin yanar gizon Sky Sports ya ruwaito.

Ana yi wa Buffon kallon daya daga cikin masu tsaron ragar da suka yi fice a duniya a wannan zamani, ida ya kafa tarihin dan wadan da ya fi kowanne taka leda a Serie A da wasanni 656.

Tun a shekarar 2001 ne Buffon mai shekara 43 ya je Juventus, inda ya ci gaba da zama gabanin komawarsa PSG a shekarar 2018.

Ya yi kakar wasa daya a PSG inda a shekarar 2019 ya sake dawo wa Juventus, kungiyar da ya lashe kofunan gasar Serie A goma da Coppa Italiya hudu.