✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan bar Liverpool a karshen kakar wasanni —Sadio Mane

Akwai alaka mai karfi tsakanin dan wasan Senegal din da FC Bayern Munich.

Sadio Mane ya yanke shawarar barin Liverpool, ya shirya komawa wata kungiyar bayan kwashe shekaru masu yawa a Anfield – amma sai nan gaba kungiyar za ta tabbatar.

Akwai alaka mai karfi tsakanin dan wasan Senegal din da FC Bayern Munich – sai dai har yanzu ba a cimma wata matsaya ba abin da zai bai wa sauran kungiyoyi damar daukar dan wasan idan suna bukata.

Dan wasan ya buga wa Liverpool wasa 269, ya kuma ci kwallo 120 ya kuma taimaka aka ci 48.

Dan wasan wanda kungiyarsa ta yi rashin nasara har sau biyu a hannu Real Madrid a wasan karshe na Kofin Zakarun Turai, ya ci kofina shida da Liverpool