✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan bayar da tallafin N7trn a kwana 100 na farkon mulkina muddin aka zabe ni – Atiku

Ya ce zai aiwatar da tsarin ne a kwana darinsa na farko

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kirkiro wani shirin bayar da tallafi da ya kai na Naira tiriliyan bakwai a kwanaki 100 na farkon mulkinsa, muddin aka zabe shi.

Ya ce shirin, na kimanin Dalar Amurka biliyan 10, zai mayar da hankali ne wajen tallafa wa kanana da matsakaitan sana’o’i.

Atiku ya bayyana hakan ne ranar Talata, lokacin da yake gabatar da manufofi da tsare-tsarensa na tattalin arziki ga Najeriya, yayin wani taron ’yan kasuwa masu zaman kansu da Kasuwar Bajekoli, ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu ta Jihar Legas (LCCI) ta shirya a Legas.

Dan takarar ya kuma ce zai yi wa tsarin tattalin arzikin kasar garambawul ta yadda zai bunkasa.

A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, zai dauki matakan gaggawa da za su taimaka wajen rage kowacce irin zirarewar kudi daga lalitar gwamnati ta ba gaira ba dalili, musamman ta wajen biyan tallafi.

Atiku ya kuma ce, “Za mu dakatar da kowanne irin bayar da tallafi ga kadarorin gwamnati, musamman wadanda kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.

“Za mu dauki matakan rage zirarewar kudade daga lalitar gwamnati, ta hanyar rage kudaden gudanar da gwamnati na yau da kullum. Sannu a hankula, za mu tabbatar cewa kudaden tafiyar da gwamnati ba su wuce kaso 45 cikin 100 ba, kuma za mu sake duba hanyoyin da ake bi wajen yin sayayya a gwamnatance, domin mu tabbatar da cewa mun toshe duk wata kofar barna.

“Za mu mayar da hankali matuka wajen fito da hanyoyin samar da kudaden shiga da ba na bashi ba, ta hanyar hadin gwiwa da ’yan kasuwa wajen gudanar da manyan ayyuka,” inji shi.

Atiku ya kuma nuna takaicinsa kan yadda kudaden da Najeriya ke kashewa wajen biyan basusussukan da ta ciyo suka zarta wadanda take samu a watanni uku na farkon 2022, inda ya yi alkawarin yi wa tufkar hanci muddin aka zabe shi.

“Za mu tabbatar cewa ko da mun ciyo bashi, mun yi amfani da shi a ayyukan da za su rika kawo wa gwamnati kudaden shiga ne su kuma bunkasa tattalin arzikin kasa,” ini Atiku.