✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan dora daga nasarorin Buhari idan na ci zabe – Tinubu

Buhari ya ce suna da kwarin gwiwar Tinubu zai lashe zaben

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin  idan aka zabe shi zai yi iyakar kokarinsa wajen dorawa kan nasarorin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu.

Ya kuma yi alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar nan da tsaro da wutar lantarki da harkokin noma da samar da ayyukan yi da bunkasar harkokin masana’antu.

Tinubu ya yi jawabin ne a yayin bikin kaddamar da yakin neman zabensa ranar Talata a babban filin wasa na Rwang Pam da ke Jos, babban birnin jihar Filato.

Tsohon Gwamnan Jihar ta Legas ya kuma kira ga ‘yan Najeriya da su lura da ’yan siyasar da za su jefawa kuri’unsu a wannan zabe da za a gudanar tare da yin watsi da marasa cika alkawuran da suka dauka.

Shugaban Kasa Muhammadu Bahari, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta kammala dukkan shirye shiryenta na lashe zaben saboda irin dimbin ayyukan alherin da suka shimfida a Najeriya.

Ya ce ganin irin goyan bayan da Tinubu ya samu yayin zaben fid-da gwanin jam’iyyar ta APC, ya nuna cewa lallai ya karbu a wajen ’yan Najeriya.

Shugaba Buhari ya yi kira ga dukkan magoya bayan jam’iyyar, su tashi su yi aiki don ganin jam’iyyar ta kai ga nasara a zaben.

Shi ma Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Alhaji Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyarsu ba ta tsoran kowace jam’iyya a zaben ganin irin nasarorin da aka samu a gwamnatin Shugaba Buhari.

Ya ce idan aka zabi Bola Tinubu, zai dora ne a kan irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na yakin neman zaben na Bola Tinubu kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce Jihar Filato ta sha shirya irin wadannan tarurka na yakin neman zabe kuma daga bisani ’yan takarar su lashe zaben.

Shi dai wannan taro, ya sami halartar Gwamnonin jam’iyyar ta APC da ’yan majalisar tarayya da na jihohi da dubban magoya bayan jam’iyyar, daga dukkan jihohin kasar nan.