✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan fallasa barayin mai duk girmansu idan na ci zabe —Atiku

Atiku ya bayyana haka ne a gaban manyan ’yan kasuwa a Legas

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin bankadowa tare da fallasa masu satar man fetur da masu daure musu gindi muddin ya zama dare shugabancin Najeriya.

Atiku ya fadi haka ne a wani taron ganawa da manya-manyan ’yan kasuwa a karkashin kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci a Legas a ranar Asabar.

Dan takarar, wanda ya bayyana takaicinsa kan yadda ake tafiyar da harkar mai a yanzu, ya ce, ba zai saurara wa masu satar shi ba da su da masu daure musu gindi duk girmansu da matsayinsu a Najeriya.

Ya kuma yi barazanar kwace duk wata rijiyar man da aka mallaka wa duk dan Najeriyan da ya ki sarrafa ta yadda ya kamata domin amfanin kasa.

“Idan har kana da rijiyar mai ka kuma ki ka sarrafa ta yadda ya kamata, za mu kwace, mu kuma ba wadanda ya kamata su aikata ta,” inji dan takarar na PDP.

Atiku ya yi wadannan kalamai ne kan abubuwan da zai aiwatar a bangaren man fetur da dangoginsa a gaban manyan attajiran da suka hada da Aliko Dangote da Tony Elumelu da Herbert Wigwe da Muhammad Hayatuddeen da sauransu, idan ya zama Shugaban Kasa.