✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan gina azuzuwa 500,000 cikin shekara 4 idan aka zabe ni — Kwankwaso

Ya ce hakan na cikin manufofin jam’iyyarsu na inganta ilimi

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin gina azuzuwa 500,000 a makarantun firamaren da ke fadin Najeriya a shekaru hudu na mulkinsa muddin aka zabe shi.

Dan takarar ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai wa Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya ranar Litinin.

Kwankwaso ya ce hakan na daga cikin kudurorin  da jam’iyyarsa ta sanya a gaba, don inganta ilimi tun daga tushe.

Ya ce, “Jam’iyyarmu ce kadai dan takararta na Shugaban Kasa ya ziyarci fiye da Kananan Hukumomi 500 da mota, don gane wa idonmu halin da jihohi da kauyukanmu ke ciki.

“Wannan ne ya sanya a dan kankanin lokaci jam’iyyarmu ta yi suna aka santa a lungu da sakon kasar nan, har muke da ’yan takara na kusan dukkanin kujerun siyasa,” in ji shi.

Kwankwaso ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi aiki tare da sarakuna, kamar yadda ya sanya su a kwamitoci na musamman na raya kasa lokacin da yake Gwamnan Kano.

A nasa bangaren, Sarkin na Zazzau Ahmad Bamalli Nuhu ya yi godiya ga Kwankwaso bisa ziyarar ban girman da ya kai masa, tare da addu’ar samun Shugaban Kasa na gari a babban zaben mai zuwa.

Sarkin ya kuma roki duk wanda ya samu nasarar zamowa Shugaban Kasa, ya kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.