✕ CLOSE Kiwon LafiyaRa’ayoyiRa'ayin AminiyaRahotoAminiyar KurmiHotunaGirke-GirkeSana'o'iKimiyya da Kere-Kere

Zan iya rasa raina wajen cika muradun magoya bayana – Obi

Najeriya za ta samu daidaito ne idan ta sauya zuwa kasa mai sarrafa abubuwa da kanta

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ce ya gwammace ya mutu da ya gaza wajen cika wa magoya bayansa burinsu.

Haka nan, Obi ya ce shugabanci na gari kadai ne zai yaye wa kasar nan matsalolin da take fuskanta tare da dora ta kan tafarkin da ya dace.

Dan takarar ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Kungiyar Editoci ta aka shirya ranar Litinin a Legas.

Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra ya ce, kasar nan tana fama da tarin matsaloli wadanda galibinsu na faruwa ne sakamakon rashin sarrafa abubuwa da kanta da ba ta yi.

Ya ce muddin kasar za ta sauya ta koma mai kokarin sarrafa abubuwa da kanta maimakon dogaro da na wasu, za a magance kashi uku cikin hudu na matsalolin da take fama da su.

A cewar Obi, rashin aikin yi da talauci da rashin tsaro na daga cikin manyan matsalolin da suka addabi kasar nan.