✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan iya tuka mota daga Abuja zuwa Kaduna babu ’yan rakiya – Ministan Buhari

Ya ce tun da wasu mutane na bi, shi ma zai iya

Minista a Ma’aikatar Kwadago, Festus Keyamo, ya bigi kirjin cewa a yanzu haka zai iya tuka mota tun daga Abuja har zuwa Kaduna ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba.

Ministan, wanda har ila yau shi ne kakakin yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels ranar Talata.

Da aka tambaye shi ko zai iya bin hanyar a mota duk da kalubalen tsaron da ke kanta, Festus Keyamo ya ce, “Tun da wasu mutanen na bi, ni ma zan iya bi. Na ga wasu labarai a makon da ya gabata da ke cewa na ce Buhari ya kawo karshen matsalar tsaro. Ni ban ce haka ba.

“Lokaci ne na sauya wa mutane magana. Ina tsokaci ne a kan abin da muka tarar a yankin Arewa maso Gabas na rikicin Boko Haram. A kan shi nake magana takamaimai ba dukkan matsalar tsaro ba, amma sai aka canza min maganar cewa matsalar tsaro nake nufi baki daya. A kan Boko Haram kawai nake magana, ban ce an kawo karshenta baki daya ba ita ma, amma an rage ta yadda ya kamata.

“Dukkan hanyoyin zuwa Chibok da na zuwa Damboa yanzu an sake bude su. Batun rikici tsakanin maonoma da makiyaya ya kai kololuwa ne tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020. Cibiyar Tattara Alkaluma kan Ta’addanci ta Duniya (GTI) ce ta fadi haka, ba ni ba.

“Cibiyar ta kuma ce lamarin ya yi matukar raguwa a 2021, haka ma a 2022, saboda haka ana samun nasara sosai.

“Amma dangane da abin da ya shafi matsalar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wannan na yarda yana karuwa a yankin Arewa maso Yamma da ma wani sashe na Arewa ta Tsakiya. Wannan babu tantama a kai,” inji Festus Keyamo.