✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Zan karasa aikin da Buhari ya fara na cefanar da NNPC — Atiku 

Ya ce yin hakan ne kadai zai sa kamfanin ya zama abin alfahari

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin in ya ci zabe zai karasa aikin da Shugaba Buhari ya fara na cefanar Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ga ’yan kasuwa.

Dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke fadin ra’ayinsa akan sauye-sauyen da gwamnati mai ci ke yi kamfanin.

Atiku ya ce yin hakan ne kadai zai sa kamfanin ya zama abin alfahari a duniya.

A ranar Talata ce Shugaba Buhari ya kaddamar da sauye-sauyen da ake yi na mayar kamfanin na kasuwanci bayan shekara 45 a matsayinsa mallakin gwamnati, kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Shugaban ya kaddamar da sauyin ne da canjin sunan kamfanin daga NNPC zuwa NNPCL.

An bikin yi bikin canjin sunan ne tare da kaddamar da sabon tambarin kamfanin a wani kasaitaccen biki a Abuja.

Sabon kamfanin zai kasance shi ne kamfanin mai mafi girma a nahiyar Africa bayan sanya hannu da shugaban kasa ya yi a kan dokar da ta kafa masana’antar man fetur.

A baya dai dan takarar na PDP ya sha fadin cewa muddin ya zama Shugaban Kasa zai sayar da NNPC ga ’yan kasuwa, amma gwamnatin ta APC ta rika sukarshi a kan lamarin.

A yanzu dai Atiku ya ce ya yi murna da cewa duk bakaken maganganun da aka fada masa, yanzu Buhari ya yi aiki da kudurinsa don neman mafita .

Ya ce yana mai fatan shi zai karasa wannan aikin da Buhari ya soma, na mayar da kamfanin daya daga cikin manya da ake ji da su, kamar kamfanin Aramco na Saudiya, da Petrobras na Brazil, idan ya zama Shugaban Najeriya a zaben 2023 mai zuwa.