✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan kawar da duk kasar da ta nemi hana ni kera makaman nukiliya – Kim Jong-un

Ya sha alwashin hanzarta kera makaman nukiliya tare da sanya su cikin shiri

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya sha alwashin hanzarta kera makaman nukiliya tare da sanya su cikin shirin fara amfani da su nan take.

Da yake magana a wajen faretin bikin
cika shekara 90 da kafa rundunar sojin kasar, Mista Kim ya yi gargadin shafe duk wata kasa da ta nemi sa-zare da
Pyongyang a kan wannan aniya.

Wakiliyar BBC ta ce hotunan da kafafen watsa labaran kasar suka wallafa sun nuna babban makami mai-linzami na kasar samfurin Hwasong-17 wanda aka kammala gwajinsa a watan jiya, bayan tabbatar da cewa zai iya kai wa kasar Amurka.

Wasu hotunan tauraron dan Adam na baya-bayan nan sun nuna cewa ana ci gaba da aikin dawo da ramukan kera makaman da aka lalata a shekarar 2017 bayan Kim Jong-un ya tattauna da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump.