✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan nuna wa gwamnati kwatar da ake yanka mutane –Turji

Kasurgumin dan ta’adda, Bello Turji, ya ce a shirye yake ya nuna wa gwamnati wasu mayanka da ake yanka ’yan uwansa a yankin da yake.…

Kasurgumin dan ta’adda, Bello Turji, ya ce a shirye yake ya nuna wa gwamnati wasu mayanka da ake yanka ’yan uwansa a yankin da yake.

A hirarsa da Aminiya a maboyarsa, Turji, wanda ya fitini jihohin Zamfara da Sakkwato, ya ce akwai mahauta akalla guda biyu da aka ware domin yanka ’yan uwansa, amma gwamnati ba ta sani ba.

Ya yi ikirarin cewa tausayin talakawa da jami’an tsaro suke kashewa ne ya sa shi rubuta wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasikar neman zaman lafiya.

A cewarsa, a baya gwamnati ta yaudare su, ta sa jami’an tsaro su kashe su, bayan ta sa sun lallashi yaransu sun mika mata makamansu da sunan zaman lafiya.

Amma duk da haka, sun zura ido su gani ko a wannan karo za ta cika alkawarin da ta yi musu domin samun zama lafiya.