✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan sa kafar wando daya da Mataimakina idan… – Gwamna Matawalle

“Kasancewar ba ma jam’iyya daya ba ya nufin ni ba mai gidansa ba ne.”

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya yi gargadin cewa zai sa kafar wando daya da Mataimakinsa, Mahdi Aliyu idan ya ci gaba da shigar masa hanci da kudindine.

An dai yi ta fuskantar yakin cacar baki tsakanin Gwamnan da Mataimakinsa tun bayan da Gwamnan ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP ya koma APC.

Sai dai yayin da Sanatoci da ’yan Majalisar Tarayya da na Jiha suka bi Gwamnan zuwa APC, har yanzu Mataimakin nasa ya ce yana nan daram a PDP.

Saboda ma ya nuna irin farin jininsa a siyasance, Mataimakin har gangami ya shirya a Jihar a makon da ya gabata.

Shirya gangamin dai ya jawo suka iri-iri, kasancewar Jihar ta fuskanci munanan hare-haren ’yan bindiga a daidai lokacin taron.

Amma magoya bayan Mataimakin Gwamnan sun ce ita ma APC ta shirya makamancin wannan gangamin lokacin da Matawallen ya koma cikinta.

Tuni dai Majalisar Dokokin Jihar ta gayyaci Mataimakin Gwamnan kan shirya gangamin, matakin da ya kara karfafa zargin da ake yi cewa tana kokarin tsige shi ne.

A yayin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na DW a ranar Asabar, Gwamna Matawalle ya ce ba zai lamunci kowanne irin nau’i na rashin da’a daga Mataimakin nasa ba.

Matawalle ya ce, “Nima ban jima da karanta labarin batun tsigewar ba, na kira wani don neman karin bayani inda yake shaida min ba za su lamunci Mataimakin Gwamna ya rika shirya gangamin siyasa a daidai lokacin da ake kashe mutane ba.

“A matsayina na Gwamnan Jihar, na yi alkawarin yin aiki tare da Mataimakina ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba, amma ba zan lamunci rashin da’a ba.

“Ba zan tsaya ina cacar baki da shi ba, amma in ya shigo gonata zan bi da shi ta hanyar da ta dace.

“Dukkanmu mun amince mu jinkirta kowanne irin taron siyasa da zai bukaci gayyato baki daga wasu jihohin, kasancewar mun rasa wasu daga cikin magoya bayanmu lokacin irin wannan taron.

“Kamata ya yi Mataimakin Gwamnan ya sanar da ni kowanne irin abin da yake kokarin yi. Kasancewar yanzu ba ma jam’iyya daya ba wai yana nufin yanzu ni ba mai gidansa ba ne. Tun da na sauya sheka ya daina mu’amala da ni,” inji Gwamna Matawalle.