Zan sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a nan gaba – Yahaya Bello | Aminiya

Zan sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a nan gaba – Yahaya Bello

    Muideen Olaniyi Da Bashir Isah

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ce zai sake tsayawa takarar Shugaban Kasa nan gaba, duk da yunkurinsa na  farko bai kai ga gaci ba.

Bollo ya bayyana haka ne ga manema labarai a lokacin da ya kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ziyar godiya a fadarsa bisa damar shiga takara da aka ba shi.

Gwamnan ya ce, shiga takarar Shugaban Kasa da ya yi a karkashin APC gwajin karfi ne kawai, tare da cewa takarar gaba za ta fi ta baya armashi.

Daga nan, ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsa, yana mai cewa da ma ita rayuwa “ta gaji nasara da faduwa.”

Kazalika, ya bukaci magoya bayan nasa da su bai wa jam’iyya mai mulki cikakken goyon baya yayin zabukan 2023.