✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan soke biyan kudin NECO da JAMB, zan dauki sojoji 750,000 —Kwankwaso

Alkawuran dan takarar shugaban kasa a Jam'iyyar NNPP kan inganta tsaro, ilimi da tattalin arziki

Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce zai soke biyan kudin jarabawar kammala sakandare da ta shiga manyan makarantu idan ya ci zaben 2023.

Tsohon Ministan Tsaron ya yi alkawarin soke kudin rajistar shiga manyan makarantu, tare da daukar sabbin sojoji 750,000 domin kara yawan dakarun Najeriya zuwa akalla miliyan daya idan ya zama shugaba kasa.

Da yake kaddamar da kundin manufofinsa a ranar Talata, Kwankwaso ya ce, ya ce gwamantinsa za ta kara yawan ’yan sandan Najeriya zuwa miliyan daya.

Ya bayyana cewa yin hakan zai taka rawar gani wajen shawon matsalar tsaro da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya, da kuma samar da aikin yu ga matasa masu kishin kasa.

“A gwamnatinmu, babu wani dalibi dan Najeriya da zai gagara rubuta jarabawar WAEC, NECO, JAMB da sauransu… saboda tsadar kudin jarabawar.

“Duk wadannan jarabawar za su koma kyauta, haka ma takardun neman gurbin shiga manyan makarantu za su koma kyauta,” in ji dan takarar.

A cewar tsohon Gwamnan Kanon, zai yi wa tsarin jarabawar gyaran fuska tare da kara wa’adin amfanin sakamakon jarabawar zuwa shekara hudu.

“A gwamnatin Kwankwaso wa’adin amfanin sakamakon jarabawar  JAMB zai koma shekara hudu kuma za a bukaci manyan makarantu su yi amfani da shi domin daukar sabbin dalibai,” in ji dan takarar.

Tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar ganin yara miliyan 20 da ke Gararamba a kan tituna a Najeriya sun koma makaranta a cikin shekara hudu.

A cewarsa, zai yi haka ne tun daga lokacin da ya hau mulki ta hanyar yin gine-gine 40 masu dauke da  ajujuwa a kowace karamar hukumar a duk shekara, a tsawon shekara hudu.

fitar da ’yan Najeriya miliyan 20 daga kangin talauci a cikin shekara hudu masu zuwa.

Ya kuma yi alkawarin yin duba na tsanani tsarin tallafin mai, wanda ya ce ke cike da almundahana, tun daga shekarun 1970 zuwa yanzu.

Sai dai bai bayyana ko za soke tsarin ba, ko zai ci gaba da shi.

A cewarsa zai yi dukkan mai yiyuwa wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar nada a kwararru a bangaren domin bullo da tsare-tsare masu ma’ana domin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa.

Ya ce zai nada kwararrun mutane masu amana su shugabanci manyan cibiyoyin gwamnati da ke samar mata kudaden shiga da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) da Ma’aikatar Kudi da ta Kasuwanci da Zuba Jari.

Bugu da kari zai nada gogaggen masanin tattalin arziki a matsayin mashawarcin shugaban kasa kan tattalin arziki.

Game da harkar noma, Kwankwaso ya ce gwamantinsa za ta mayar da hankali kan bunkasa harkar noman zamani da kuma raya hukumar kasuwancin amfanin gona domin ganin ’yan kasuwa ba su yi wa manoma kafar ungulu ba.

A cewarsa, zai sauya fasalin Najeriya domin samar da jagororin na gari, alkinta arzikin kasa da kuma kawo cigaba mai ma’ana.