✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan tabbatar mabukata sun samu tallafin gwamnati – Sanata Laah

Sanata mai wakiltan shiyyar Kudancin Kaduna, Dakta Danjuma Tella Laah ya ce yana kan kokarinsa a halin yanzu don ganin mabukatan da ke yankinsa sun…

Sanata mai wakiltan shiyyar Kudancin Kaduna, Dakta Danjuma Tella Laah ya ce yana kan kokarinsa a halin yanzu don ganin mabukatan da ke yankinsa sun samu tallafin gwamnatin tarayya na Naira dubu biyar-biyar da take turawa ta asusun ajiyar mutum.

Sanata Laah ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da kayan tallafi da ya kawowa al’ummar shiyyarsa da ya kunshi kananan hukumomi takwas na kudancin Kaduna.

Sanatan, ya bayyana cewa duk da gwamnatin tarayya tana kan bin shirin ne cikin matakai, amma tuni ya gana da Ministar Kula da Ayyukan Jinkai da Ci gaban Al’umma, Hajiya Sadiya Umar Faruk kan batun.

“Don haka ina kira ga jama’ar shiyyata da su kara hakuri domin talakawa daga cikinsu za su amfana daga tallafin.”

Sanatan ya kuma bukaci wadanda alhakin rabon kayayyakin ya rataya a wuyansu da su tabbatar sun bi dukkanin tsarin da aka gindaya da samar da hakikanin manufar tallafin.

Tallafin zai ragewa mutane halin radadin da suka shiga a sanadiyyar annobar coronavirus da ke addabar duniya.

“Za mu yi amfani da shugabannin addinai na da shugabannin al’umma don ganin abin ya kai dukkanin gundumomi 87 da ke kananan hukumomi takwas da muke da su a shiyyar.” In ji shi.

A karshe ya shawarci jama’a da su ci gaba da kiyaye dokokin gwamnati da kuma shawarwarin jami’an kiwon lafiya don takaita yaduwar cutar a cikin jama’a.

Kayayyakin da aka raba sun hada da: buhunan gero 100 da buhunan 50 na sukari sai buhunan wake guda 804, da masara buhuna 458 da shinkafa buhu 606 sai kuma katon 3,500 na taliyar Indomie da kuma doya.

Lokacin da ake rabon tallafin