✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan Tona Asirin Wike Idan… —Dogara

Wike ya ce hujjarsa ita ce matsayar Dogara ta baya ta goyon bayan shugabancin Najeriya ya koma hannun ’yan Kudu.

Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya ce idan Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas bai daina sukar sauya shekarasa zuwa PDP ba, zai tona asirinsa duniya ta sani.

Dogara ya maida martanin ne bayan kalaman da Wiken na ranar Litinin, da ya ce dawowar tsohon shugaban majalisar zuwa PDP da mara wa Atiku baya, ha’incinsa  karara.

Wike ya ce hujjarsa ita ce la’akari da matsayar Dogara ta baya cewa yana goyon bayan shugabancin Najeriya ya koma hannun ’yan Kudu.

Sai dai wadannan kalamai ba su yi wa Dogara dadi ba, inda ya garzaya shafinsa na Twitter da martanin cewa zai fallasa maganar da suka yi da Wiken kan makamancin wannan batu.

“Dan uwana Gwamna Nyesom Wike, wace larurar kake fama da ita da ka rude haka? Ban yi tunanin ta yi tsanani haka ba,” in ji Dogara.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan ya isa abin takaici, musamman idan ka tuna hirar da muka yi da kai har muka kai ga cimma wata yarjejeniya.

“Ba zan taba cin amanar dan uwana ba, shi ya sa ba zan biye maka mu yi cacar baki a talabijin ba.

“Abin da hirarmu ta kunsa sirri ne, amma idan kana ganin sanar da duniya ba komai ba ne, to ka sanar ni a rubuce cewa kan amince, don alkalancin wanda ke da gaskiya tsakanina da kai. Alhamdulillahi ina da sahihan shaidu.”