✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan tsaya takarar gwamnan Filato a 2023 —Sonnie Tyoden

Mataimakin gwamnan ya ce zai dora daga inda Simon Lalong ya tsaya.

Mataimakin Gwamnan Jihar Filato, Sonnie Tyoden ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar don cin gajiyar kujerar Gwamna Simon Bako Lalong a 2023.

Tyoden ya bayyana haka ne a Jos a ranar Alhamis, inda ya shaida wa shugaban jam’iyyarsu ta APC na jihar, Honarabil Rufus Bature burinsa na zama gwamna a jihar.

Ya ce yana da burin dorawa daga inda uban gidansa gwamna Lalong zai tsaya da mulki.

Haka kuma ya ce yana alfahari da irin ci gaban da suka samar wa Jihar Filato tsawon lokacin da suka shafe suna shugabancin Jihar.

“Na tabbatar ina da gogewar da zan ja ragamar shugabancin Jihar Filato, saboda mun kwashe shekara bakwai a kan mulki wannan ya ba ni damar sanin makamar aiki.

“Burin jam’iyyarmu shi ne fadada ayyukan da gwamna Simon Lalong zai bari don amfanar jama’ar jihar nan, zan tabbatar da hakan da zarar na samu wannan dama.

“Shugabancin Jiha kamar Filato na bukatar jagora mai gogewa da jajirwa da kuma dabarun mulki, ina da yakinin ina da wannan nagartar.

“Wannan shi ne abin da wannan gwamnati ta samar a Filato kuma ina fatan dorawa tare karawa daga inda ta tsaya, musamman dangane da abin da ya shafi hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar nan,” in ji shi.