✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan tsaya wa Nnamdi Kanu —Soludo

Matsalar tsaron Kudu maso Gabas na da alaka da kungiyar IPOB.

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya saki shugaban kungiyar ’yan awaren Biafra ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Gwamnan ya ce a shirye yake ya tsaya wa Nnamdi Kanu wanda ke hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), matukar gwamnati za ta sake shi.

Mista Soludo ya yi kiran ne a lokacin gangamin yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APGA, Farfesa Peter Umeadi da aka gudanar a Akwa, babban birnin jihar.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce matsalar tsaron da yankin Kudu maso Gabashin kasar ke fuskanta na da alaka da manyan jagororin kungiyar IPOB.

Don haka a cewarsa, dole ana bukatar jagororin IPOB a teburin tattaunawar sulhu tsakanin gwamnati da kungiyar.

A ’yan kwanakin nan ne dai wasu rahotanni sun bayyana yadda mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, wato tsohon gwamnan Jihar Abia, Orji Kalu na cewa shi ma zai tsaya wa jagoran ’yan awaren domin a sake shi.