✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanen Barkwanci: ‘Buhari’ ya aike wa Bulama sako

Mako guda bayan zanen Daily Trust ya tayar da kura, 'Buhari' ya yi wa Bulama sako

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika wa mai zanen barkwancin siyasa na kafafen Aminiya da Daily Trust, Mustapha Bulama, sako domin nuna masa ayyukan da gwamntinsa ta yi.

Kungiyar Yada Labaran Buhari a cikin sakon ta shaida wa mai zanen barkwacin cewa tana so ne ta aika masa da kundayen bayanan ayyukan gwamnatin Buhari domin ya gani.

“Zuwa ga Bulama, Muna da kwafin dukkannin wadannan kundayen bayanai da Tawagar Watsa Labarai ta Fadar Shugaban Kasa ta hada. Za mu so sanin inda kake so a kai maka su. Na gode”, inji sakon Kugiyar Shugaban Kasar ga Bulama, kamar ta wallafa a shafinsa ta twitter.

Mustapha Bulama ya amsa wasikar da cewa, “Ku tura zuwa ofishin Daily Trust… Zan yi matukar farin cikin samun su. Na gode. Ina fata kun ga zanen barkwancin da na yi jiya”.

– Zanen Bulama ya tayar da kura –

Sakon na ‘yan Buhari na zuwa ne kasa da mako guda bayan wata zanen barkwancin da Bulaman ya yi kan bikin daurin auren diyar Buhari Hanan ya dayar da kura.

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bakin mai magana da yawunta ta ce zanen bai yi mata adalci ba, kamar yadda Mai Magana da Yawunta, Barisa Aliyu Abdullahi ya bayyana.

A zanen wanda ya karade shafukan zumunta, an ga Aisha ta daga hoton daurin auren tana nuna wa ’yan Najeri da aka gani suna nutsewa a cikin koramar talauci.