✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga ta barke kan umarnin jingine wa’adin tsofaffin kudi

Masu zanga-zangar na cewa hukuncin wata manakisa ce ta sayen kuri’u a Zaben 2023.

Daruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar kin amincewa da umarnin da kotun koli ta bai wa Babban Bankin Najeriya (CBN) na dakatar da ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin wa‘adin daina karbar tsofaffin takardun kudi.

Masu zanga-zangar sun taru a shalkwatar CBN da ke Abuja, inda suke ikirarin masu sayen kuri’a ne kadai ke kokarin amfani da kotun don biyan bukatarsu.

Mutanen dai rike da takardu da allunan masu rubutun cewa: “makiya sababbin takardun kudi su ne masu sayen kuri’a da kuma ‘yan bindiga.

“Shugaba Buhari masu kin kundirin nan na shirya manakisar hana Zaben 2023 ne, kada ka bar su su yi nasara.”

A wannan Larabar ce Kotun Kolin Najeriya ta dakatar da Gwamnatin Tarayya daga aiwatar da wa’adin amfani da tsoffin takardun kudin kasar.

Hukuncin Kotun na zuwa ne bayan da Babban Bankin Najeriya CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsoffin takardun 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sauyawa fasali.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnoni uku ne dai da suka hadar da na Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da karar a gaban Kotun Kolin suna kalubalantar wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin.

A hukuncin wucin-gadin da suka suka yanke, alkalan kotun bakwai karshin jagaorancin Mai Shari’a John Okoro, sun dakatar da Gwamnatin Tarayya da CBN da sauran bankunan kasuwanci na kasar daga aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kudin kasar.

Kotun ta kuma ce dole ne Gwamnatin Tarayya da CBN da kuma sauran bankunan kasar su jingine batun aiwatar da wa’adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin ranar 15 ga watan Fabrairu.