✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zanga-zanga: ’Yan fansho sun tare Gidan Gwamnatin Gombe

Shekara tara Gwamnatin Gombe ba ta biya tsoffin ma’aikata kudadensu na giratuti.

’Yan fansho sun yi cincirindo inda suka tare hanyar Gidan Gwamnatin Jihar Gombe don neman a biya su hakkokinsu na fanso da giratuti.

Cincirindon ’Yan fanshon da suka hana shige ko fice tare da gurgunta harkoki a Gidan Gwamnatin Jihar, sun ce ba za su tashi ba sai sun damka wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya takardar korafinsu.

“Mamabobin ba sa iya sauke nauyin da ke kansu na ciyarwa, magani, kudin makaranta, kudin haya da kudin asibiti; Hakan bai dace ba, kuma bai kamata ya ci gaba ba saboda hakkokinsu ne,” inji Shugaban Kungiyar ’Yan Fansho ta Najeriya reshen Jihar Gombe, Muhammad Abubakar.

Da yake jagorantar zanga-zangar lumanar, Shugaban Kungiyar ya ce har yanzu Gwamnatin Jihar ba ta biya ma’aikatan da suka yi ritaya shekara tara da suka wuce kudaden su na giratuti ba.

Ya kara da cewa tsawon shekara hudu ke nan Gwamnatin ba ta biyan tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi kudadensu na fansho.

Dattawan na kuma bukatar a sanya ma’aikata 700 na kananan hukumomi da suka yi ritaya shekara biyu da suka wuce cikin jerin masu karbar fansho.

Zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto, baya wani jami’in gwamnatin jihar ko gwamnan da ya fito domin ganawa da dattawan.