✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar EndSARS: Wata dama da aka rasa

Duk shaidun da ake da su zuwa yanzu suna nuni da cewa babu asarar rai ko daya.

Najeriya ba ta taba rasa damar da za ta rasa ba. A farkon watan Oktoban bara, dubban matasan Najeriya maza da mata ne suka yi dafifi a kan titunan Legas da Abuja da sauran garuruwa da dama don nuna adawa da abin da suka kira cin zarafin da ’yan sanda ke yi wa al’umma.

Zanga-zangar an shirya ta ce kan irin cin kashin da rudunar ta musamman da ke yaki da ’yan fashi da makami (SARS) ta Rundunar ’Yan sandan Najeriya ke yi.

An kafa Rundunar SARS ce a 1992 domin yaki da matsalar fashi da makami a fadin kasar nan a lokacin.

Ba da jimawa ba, wannan runduna ta rikide zuwa wani sashi na musamman da ake zargi da cin zarafin al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba da kuma karbar kudi da azabtarwa da ma kisan gilla ga ’yan Najeriya marasa laifi.

A rahoton da Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (Amnesty) ta rubuta a watan Yuni 2020 ya ce “Akalla shari’o’i 82 na azabtarwa da cin zarafi da kuma hukuncin kisa daga SARS,” a jihohi biyar a tsakanin Janairu 2017 da Mayu 2020 aka samu.

Wadannan abubuwa da ’yan sanda suka yi na zalunci sun kasance sau da yawa don neman bayanai ko kuma tilasta a yi ikirarin aikata laifi, wanda da yawa wadanda aka kashe ba su aikata laifuffukan ba.

Rahoton ya ce wadanda wannan lamarin ya rutsa da su, galibinsu matasa ne ’yan Najeriya da ke tsakanin shekara 18 zuwa 35 kuma mafi yawa daga cikinsu talakawa ne.

Hakazalika rahoton ya gano cewa yawan azabtarwa da SARS ke yi, ya sa mafi yawancin ofisoshin ’yan sanda a fadin kasar nan suka ware wani daki a matsayin na azabtarwa da tsoratarwa.

Don haka matasan masu zanga-zangar da suka fito kan tituna suna da tabbatacciyar hujja.

Kuma sama da mako biyu suka dauka don matakin ganin lamarin ya gama gari irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a Najeriya.

Sun yi haka ne ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta wajen shirya taron, inda suka bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta sakin duk masu zanga-zangar da aka kama; a yi adalci ga duk wadanda suka mutu sakamakon zaluncin ’yan sanda ta hanyar biyan iyalansu diyya da bincike da kuma gurfanar da duk masu hannu a kararrakin da aka ruwaito na zaluncin ’yan sanda a cikin kwana 10 kuma a tarwatsa SARS tare da yin bincike na natsuwa a kan jami’an kafin a sake tura su, kuma a kara wa ’yan sanda albashi.

Zanga-zangar ta yi tasiri sosai cikin gaggawa, Shugaba Buhari ya ba da umarnin rusa Rundunar SARS tare da amincewa da korafe-korafen masu zanga-zangar.

“Zan so in yi amfani da wannan dama domin in nuna damuwata a kan wannan zanga-zanga da ’yan Najeriya ke yi a baya-bayan nan game da yadda ake amfani da karfi fiye da kima a wasu lokutan ma har da kashe-kashe ba tare da shari’a ba da kuma halin da bai dace ba na ’yan sandan Najeriya.

“Rusa Rundunar SARS shi ne mataki na farko a kudirinmu na aiwatar da sauye-sauye a rundunar ’yan sanda domin tabbatar da cewa aikin farko na ’yan sanda da sauran jami’an tsaro ya kasance kare rayuka da rayuwar jama’armu,” inji shi.

Sai dai jim kadan zanga-zangar ta canja sabon salo, inda daruruwan ’yan iska suka auka wa masu zanga-zangar a Abuja da Legas, yayin da a jihohin Edo da Ondo, masu zanga-zangar suka shiga gidan yari suka sako fursunoni sama da 2,000, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

Fiye da wannan, masu zanga-zangar sun fara neman rusa gwamnati da kiran Shugaban Kasa ya yi murabus.

Duk da haka, mafi munin lamarin ya kasance a ranar 20 ga Oktoba, bayan da jami’an tsaro suka auka wa masu zanga-zangar a harabar Lekki Toll Gate, don wargaza su.

Shin an samu ‘kisan kai’ na masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate ranar 20 ga Oktoba 2020?

Duk shaidun da ake da su zuwa yanzu suna nuni da cewa babu asarar rai ko daya.

A wani rahoto da Legas ta fitar a lokacin ya ce mutum biyu sun rasa rayukansu a wannan rana.

Tun daga wancan lokaci, masu zanga-zangar, ko iyalansu, ko kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula da suka sa-ido sosai a kan zanga-zangar ba su fito da ko da ’yar alamar ‘kisan kai’ ba.

Tun farko dai Kungiyar Amnesty ta yi ikirarin cewa an kashe mutum 56.

Yanzu kuma ta ce wadanda suka mutu a wannan rana ‘akalla mutum 12 ne’.

Don haka, yana da kyau ta kawo hujja a kan wannan ikirarin nata.

Muna da yakinin cewa dagewa kan labarin karya na “Kisan Lekki” shi ne babban dalilin da ya sa aka dakile nasarorin da #EndSARS ta samu.

Muna kira ga matasa su mayar da hankali wajen tabbatar da bukatunsu kada su rika wuce gona-da-iri, kamata ya yi su samar da wata kungiya ta siyasa wacce za ta iya canja tsarin a zaben 2023 mai zuwa.