✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar iyalan fasinjojin jirgin kasan Kaduna da ke hannun ’yan bindiga

Iyalan ragowar fasinjojin jirgin kasan Kaduna da ’yan ta’addan IS suka sace guda 50, sun gudanar da zanga-zangar luman a Jihar  Kadunan ranar domin nuna…

Iyalan ragowar fasinjojin jirgin kasan Kaduna da ’yan ta’addan IS suka sace guda 50, sun gudanar da zanga-zangar luman a Jihar  Kadunan ranar domin nuna rashin jin dadinsu bisa yadda gwamnati ke tafiyar hawainiya wajen kubutar da ’yan uwansu daga hannun ’yan bindigar.

Iyalan sun fara zanga-zangar ne da karfe 7:30 na safe, kuma tare da mutane da dama, inda suka durfafi Gidan Nagwamatse da ke kan Titin Akilu da ke garin Kaduna.

Masu zanga-zangar sun daga kwalaye da takardu dauke da rubutun da ke cewa “Ku sakar mana ’yan uwanmu”.

Dokta Abdulfatai Jimoh shi ne shugaban kungiyar iyalan, ya kuma bayyanawa wakiliyarmu cewa kiran da suke wa gwamnati da babbar murya ba zai kare ba, ta taimaka ta yi duk mai yiwua domin karbo musu ’yan uwansu da gaggawa.

Ya ce, “Mu ’yan kasa ne da ke da ’yancin zuwa duk inda muke so kuma hakkin gwamnati ne ta ba mu tsaro, don haka muka mika kawunanmu da lamarin tsaronmu ga gwamnati , domin aikinta ne.”