✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar iyayen Daliban Afaka a Abuja

Suna neman dauki domin a ceto daliban da aka sace tun a watan Fabrairu

Iyayen dalibai 39 da aka sace a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka, Jihar Kaduna sun yi zanga-zanga a Abuja don neman a kubutar da ragowar daliban 29 da suka rage a hannun ’yan bindiga.

Sun yi zanga-zangar ne tare da kungiyar daliban kwaleijin, kwanaki kadan bayan ’yan bindiga sun yi barazanar kashe ragowar daliban da suka sace daga Jami’ar Greenfield da ke Jihar, idan ba a biya kudin fansa ba.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta lashi takobin rashi tattaunawa ko biyan kudin fansa ga ’yan bindiga.