✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar Zakzaky: IMN ta maka Shugaban ’Yan Sanda a kotu

IMN ta maka Shugaban ’Yan Sanda da na Babban Asibitin Kasa a kotu, kan rike gawarwakin mambobinta masu zanga-zangar neman a saki Zakzaky

Kungiyar mabiyar akidar Shi’a a Najeriya (IMN) ta maka Shugaban ’Yan Sanda da na Babban Asibitin Kasa a kotu, kan rike gawarwakin mambobinta da ’yan sanda suka bude wa wuta a yayin zanga-zanga a Abuja.

IMN ta shigar da karar ne zargin su da kin sakin kagawarwakin mambobinta guda tara kamar yadda Mai Shari’a Taiwo O. Taiwo na Babbar Kotun Tarayya da Abuja ya umarta a ranar 29 ga watan Yuni, 2022.

Kakakin majalisar malaman IMN, Halima Aliyu, ta sanar a ranar Litinin, cewa, “Shugabannnin biyu sun bijire wa umanin kotu kuma za su gurfana a gaban Mai Shari’a J. K. Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja ranar Laraba, 5 ga Oktoba, 2022”.

Ta ce an kashe mabiya Shi’a 9 ne bayan bayan ’yan sanda sun bude wuta sun kashe mutum 12  a lokacin IMN ta gudanar da muzaharar neman a sako jagoransu a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzakiy a 2019.

Ta ce sauran mutum uku da suka rasu bayan ’yan sanda sun bude wuta sun hada da wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da dan jaridar gidan talabijin na Channels da wani mutun da ba a san kowane ne ba.

Ta bayyana cewa bayan lamarin, ’yan sanda sun kwashe gawarwakin inda suka kai hudu Babban Asibitin Kasa, biyu a Asibitin Asokoro, duk da cewa masu zanga-zangar sun dauke ragowar gawarwaki shida.

A cewarta, ranar 29 ga Yuni, 2022, kotu ta umarci Shugaban ’Yan Sadan Najeriya da ya biya diyyar Naira miliyan 15 ga iyalan mamatan, tare umartar Babban Asibitin Kasa ya mika musu su gawarwakin, amma har yanzu hakan ba ta samu ba.

Shi ya sa, a cewarta, IMN ta shigar da kara “zargin yi wa umarnin kotu karan tsaye a kan Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da kuma Shugaban Babban Asibitin Kasa da ke Abuja.”

Halima ta ce, “Daga cikin masu zanga-zangar da ’yan sanda suka tsare, ba tare da ba su kulawa, mutum uku sun rasu, wadanda su ma aka kai gawarwakinsu zuwa Asibitin Asokoro.

“Har yanzu akwai gawarwakin mutum biyar a Asibitin Asokoro da wasu hudu a Asibitin Kasa, kuma duk kokarin da muka yi na karbar su, ba mu samu hadin kai daga hukumomin asibitin da na ’yan sanda ba,” in ji ta.