✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Jos za ta binciki masu gadin ta kan zargin muzguna wa dalibanta

An dauki matakin ne bayan wani faifan bidiyon zargin cin zarafi ya bulla

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ta kafa wani kwamiti don gudanar da bincike kan zargin muzguna wa dalibai da ake zargin masu gadin jami’ar na yi.

Mataimakin Rijistaran Jami’ar Kan Sha’anin Yada Labarai, Abdullahi Abdullahi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis a Jos, babban birnin Jihar.

Abdullahi ya ce an ga wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta na zamani wanda ke nuni da yadda wani mai gadin jami’ar ke muzgunawa wani dalibi.

“Hankalin Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Jos ya kai kan wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta na zamani mai nuni da yadda wani mai gadin jami’ar ya muzguna wa wani dalibi,” inji shi.

Haka nan, ya ce an gano dalibin da lamarin ya shafa mai suna Ponsel Dashe, wanda dan aji biyu ne a Sashen Koyon Aikin Jarida na jami’ar.

A cewar jami’in, ganin faifan bidiyon ne ya sanya Hukumar Jami’ar yanke shawarar daukar matakin bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin da kuma hana aukuwar hakan a gaba.

(NAN)