✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin fyade: An gurfanar da korarren dogarin Zazzau a kotu

Budurwar da aka yi wa fyaden dai ta je neman taimako ne Fadar Sarkin Zazzau

Yan sandan a Zariyan Jihar Kaduna sun gabatar da korarren dogarin Masarautar Zazzau da wasu mutum hudu a gaban kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Chediya, bisa zargin aikata fyade.

Mai gabatar da kara, Sufeto Mannir Nasir Dayi, ya shaida wa kotun cewa a ranar 9 ga watan Janairun 2023 wani mai suna Malam Ibrahim Kabiru ya kai kara ofishin ’yan sanda da ke kofar Fada Zariya, cewa wata yarinya ta je Fadar Zazzau ganin Sarki don neman taimakon auren da za ta yi.

Daga nan sai wani Dogari mai suna Samaila Abubakar da yake unguwar Rimin Tsiwa a Zariya ya yaudare ta da niyyar taimaka mata, inda ya kai ta wani daki kuma daga bisani suka yi lalata.

Hakan, a cewar mai gabatar da karar, ya saba wa sashi na 59 da 368 Kundin Dokokin Jihar Kaduna.

Ana zargin dogarin da aikata laifin ne tare da wasu mutum hudu.

Bayan karanta karar a gaban kotu, sai alkali ya tambayi wadanda ake tuhuma ko sun yarda da tuhumar da ake musu?

A nan ne shi wanda ake tuhuma na farko ya amsa laifin, ragowar kuma suka ki amincewa da tuhumar da ake musu.

Daga nan ne lauyan wadanda ake kara, Abubakar Ishak, ya roki kotun da ta ba da belin wadanda ake tuhuma, a bisa dogaro da sashi na 36 (5) wadda bai hana a ba da bilinsu ba.

Sai dai mai gabatar da kara ya roki kotu da kada ta bayar da belin au, saboda dalilai na rashin tabbas da kuma yanayin yadda aka aikata laifin.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Abubakar Aliyu Lamido, ya ki amincewa da rokon lauyan wadanda ake kara, inda ya ba da umurnin a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu na wannan shekarar.