✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin aikata laifi: ’Yan sanda sun bajekolin mutum 156 a Kano

Laifukan da ake zarginsu sun hada da garkuwa da mutane satar shanu, satar motoci, damfara, daba, safarar miyagun kwayoyi.

’Yan sanda a Jihar Kano a ranar Juma’a sun bajekolin kimanin mutum 156 da suka kama a sassa daban-daban na Jihar bisa zargin aikata laufukan da dama.

Daga cikin laifukan da ake zargin mutanen da aikatawa akwai garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, satar shanu, satar motoci, damfara, daba, safarar miyagun kwayoyi da dai sauransu.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Sama’ila Dikko ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a, inda ya ce ana zargin 18 daga cikinsu da fashi da makami, takwas kuma garkuwa da mutane, 10 satar shanu, bakwai safarar miyagun kwayoyi sai kuma mutum 13 da ake zargi da satar motoci.

Kwamishinan ya kuma ce akwai mutum biyar da ake zargi da aikata damfara, yayin da 99 kuma suka shiga hannu bisa zargin aikata daba.

Ya kuma ce rundunar ta sami nasarar ceto mutum 14 daga hannun masu garkuwa da mutane  a fadin Jihar.

Wasu matasa da aka kama da makamai da sauran kayan laifiWasu matasa da aka kama da makamai da sauran kayan laifi
Wasu matasa da aka kama da makamai da sauran kayan laifi

“Kazalika, mun kwato bindigogi guda 10, motoci 16, babur din Adaidaita Sahu 16, babura, shanu biyar, wukake 76, wayoyin salula 34, na’urar sanyaya daki guda biyar da kuma kunshin Tabar Wiwi guda biyar wacce darajarta ta kai kusan Naira miliyan biyu,” inji Kwamishinan.

Daga cikin wadanda ake zargin har da wani matashi, Benjamin Oguchukwu, mai kimanin shekara 24 wanda ake zargi da zama dilan Hodar Iblis wanda aka kama a unguwar Badawa Layout da ke Kano.

Wanda ake zargin dai ya amsa cewa ya kan sayar da akalla kilogiram daya na hodar a kullum.

Bugu da kari, rundunar ta kuma kama wani mai suna Magaji Adamu wanda ya yi barazanar sace wani mutum a kauyen Gidan Doka da ke Karamar Hukumar Sumaila a Jihar muddin bai bashi Naira miliyan biyu ba.

Tuni dai wanda ake zargin da kuma wayar day a yi amfani da ita wajen yin kiran suka shiga hannu.

Kwamishinan ’yan sandan ya kuma ce rundunar ta sami damar kai samame maboyar masu aikata laifi da dama a Jihar sakamakon bayanai da kuma hadin kan da take samu daga jama’ar gari.