✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin badala na neman karya arzikin Bill Gates

Ana ganin lamarin ka iya shafar rayuwar attajirin da ma tattalin arzikinsa.

Jaridar Wall Street Journal, ta rawaito cewa shahararren attajirin duniya, Bill Gates ya bar shugabancin kamfanin Microsoft a bara ne sakamakon wani bincike da aka yi a kansa kan zargin yana soyayya da wata ma’aikaciyar kamfanin, halayyar da ake ganin hakan bai dace ba sam.

A cikin wata sanarwa da wani mai magana da yawun kamfanin Microsoft din ya fitar, ya ce a cikin shekarar 2019, a kamfanin an samu wata ’yar matsala da Gates din saboda ya kulla wata kyakkyawar alaka da wata ma’aikaciyar kamfanin a shekara ta 2000.

Mai magana da yawun Gates ya tabbatar da cewa, “babu wani abu mara kyau da ya faru tsawon shekaru 20 da suka gabata kuma maigidana ya kare aiki cikin aminci.

“Yanke shawarar ajiye mukaminsa ba shi da wata alaka da wani abu, sabanin abubuwan da mutane ke zuzutawa.”

Gates ya ce, “A shekarar da ta gabata na sauka daga kan mukamina ne don in samu cikakken lokaci saboda in tunkari abubuwan da ke gabana na jama’a.”

Sai dai Jaridar New York Times, a rahoton da ta fitar ranar Lahadin da ta gabata ya ambato jerin sunayen wasu mutanen da ke da masaniya kai tsaye dangane da halayyar Bill Gates, inda ta ruwaito cewa yana da alaka da wata mata ma’aikaciya da ke masa aiki a kamfanin Microsoft da kuma Gidauniyar Bill da Melinda Gates, inda mutane suka bayyana abun a matsayin mara dadin ji saboda rashin dacewar aikata hakan.

Ita ma kafar yada labarai ta NBC ta tabbatar da wannan labarin, inda a gefe guda mai magana da yawun Gates ya bayyana cewa, “ikirarin cin zarafin ma’aikaciya da ake wa mai gidana labarin kanzon kurege ne.”

A cikin shekaru 10 da suka gabata, Bill Gates ya yi kokari wurin kyautata rayuwar mutane da dama, inda ya yi suna a duniya a matsayin mai hangen nesa.

Ya yi kokari wajen jawo hankali da wayar da kan mutane sosai kan cutar COVID-19 da ta gallabi duniya.

Bayan fitar wani rahoto da yake cewa Bill gates din, wanda shi ne ya kafa kamfanin Microsoft tare da hadin gwiwar matarsa, Melinda French Gates, wanda aurensu ya mutu bayan sun kwashe kimanin shekaru 27 tare.

Fitar wannan labarin ya tayar da hankalin makusantansa da manyan mutane a duniya, ya kuma sanya ayar tambaya dangane da rayuwarsa.

Mutanen da dama na ganin wannan lamarin ka iya shafar rayuwar attajirin da ma tattalin arzikinsa, duk a sakamakon wannan lamari da ya samu kansa a ciki.