✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin batanci: Abduljabbar ya nemi a sauya masa kotu

Sheikh Abduljabbar ya zargi alkalin kotun Musulunci da dakile shi.

Malamin nan da ake zargi da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi Shugaban Alkalai na Jihar Kano, Dokta Tijjani Yusuf Yakasai ya sauya masa kotun da ke sauraren shari’arsa.

Abduljabbar ya nemi sauyin kotun ne saboda zargin rashin ba shi cikakkiyar damar kare kansa da alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola yake yi.

Abduljabbar Kabara ya bayyana hakan ne a zaman kotun na ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.

Ya gabatar da bukata ce bayan da kotun ta nemi sanin dalilin da ya hana lauyansa halartar zaman kotun.

Da yake karin haske game da dalilansa na neman canjin kotun, Abduljabbar Kabara ya shaida wa kotun cewa ya rubuta wa Shugaban Alkalan Jihar takardar neman a canza masa kotu saboda rashin gamsuwarsa da yadda shari’ar ke tafiya da kuma yadda alkalin kotun yake da alaka da wasu bangarorin da ke karar sa.

“Na farko alkalin kotun nan ya hana ni damar yin bayanan kariya yadda ya kamata.

“A lokacin da na fara karanta litattafaina sai aka rika katse ni aka hana ni damar yin cikakken bayani a kan wasu soke-soke da na shiryo wadanda suke da dangantaka da cajin da ake yi min, wanda a wancan lokacin shi kansa lauyana, Barista Ambali Mohammed (SAN) ya goyi bayan hana ni wannan damar daga kotun.”

Har ila yau Abduljabbar Kabara ya zargi kotun da musanya masa bayanansa da ake rubutawa, wanda a cewarsa, har sai da ya ja hankalin alkalin a kan hakan kafin daga bisani aka gyara.

“A lokuta da dama na sha ganin ana musanya min maganganuna ko kuma a rage min su a cikin littafin daukar bayani na kotun wanda na taba jan hankalin alkalin a kan hakan har kuma aka yi gyara.”

Haka kuma Abduljabbar Kabara ya zargi alkalin da hana lauyansa damar tsoma baki a shari’ar a lokacin zaman kotun na baya lamarin da ya fusata lauyan ya fice daga kotun.

Karin bayani na tafe