✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin batanci: Lauyan Abduljabbar ya nemi kotu ta yi watsi da karar gaba daya

Ya ce tuhumar da ake wa malamin babu ita a doka

Lauyan da ke kare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a shari’ar da ake masa kan zargin aikata batanci ga Annabi (S.A.W) Barista Dalhatu Shehu Usman, ya roki kotun da take sauraron karar da ta yi fatali da ita gaba daya.

Ya yi rokon ne a yayin zaman kotun ta Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a ranar Alhamis.

Lauyan ya yi rokokn ne bisa dogaro da cewa cajin da ake yi wa wanda ake kara bai inganta ba, saboda sashen da suka yi dogaro da shi ya saba da cajin da ake tuhumarsa da shi.

Kotun dai, karkashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta sanya ranar bakwai ga watan Yulin 2022 don yanke kwarya-kwaryar hukunci kan ko za ta kori shari’ar ko kuma a’a.

Barista Dalhatu ya ce, “Idan an duba dukkanin cajin da masu kara ke tuhumar wanda ake kara ya dogara ne a kan sashe na 382 na Penal Code wanda ke magana a kan yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

“Sai dai kuma idan an duba tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda ake kara ana cewa ya yi wa Bukhari da Muslim batanci. Wanda kuma wancan sashen ya yi magana ne akan yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) kawai.”

Barista Dalhatu ya kara da cewa, “Ana cajinsa da laifin da ba ya cikin rubutattun laifuka wannan kuma abu ne da ya saba da sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyara wanda ya ce ba a cajin mutum da laifin da ba a ambace shi ko hukuncinsa a cikin kundin laifuka ba.”

A cewar Barista Dalhatu, don haka yake neman kotu da ta sallami wanda ake kara tare da umartar Gwamnatin Jihar Kano da ta nefi afuwarsa.

Tunda farko a zaman kotun, lauyan gwamnati, Dokta Abdurrahman Ahmad, ya jagoranci yi wa wanda ake kara tambayoyi inda kuma ya amsa wasu tare da kin amsa wasu tambayoyin.

Daga nan ne lauyan ya nemi kotu da ta sanya wata rana da za a sake komawa don ci gaba da yin tambayoyi ga wanda ake karar.

Idan za a iya tunawa, tun a watan Yulin shekarar 2021, Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotun bisa zargin yin batanci ga Annabi (S.A.W) da tayar da hankulan jama’a.