✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin batanci: Legal Aid ta ce ba za ta iya ba Abduljabbar kariya ba

Abdulabbar ya ki aminta da lauyan gwamnati, kotu ta umarci Dalhatu Usman ya ba shi kariya

Hukumar Agaza wa Shari’a ta Kasa (Legal Aid Council) ta bayyana cewa ba za ta iya bai wa Sheikh Abduljabbar Kabara kariya a shari’ar da ake masa ba.

Ana zargin Abduljabbar Kabara da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da da kuma tayar da hankulan jama’a.

Hukumar ta Legal Aid ta bayyana haka ne a cikin wata takardar da ta aike wa Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano bayan da kotun  ta umarci Hukumar da ta ba wa Abduljabbar Kabara lauyan da zai tsaya masa.

Daraktan Hukumar a Jihar Kano, Barista Mukhtar Labaran Usman, ne ya bayyana cewa Hukumarsu ba ta tsaya wa mutumin da abin da yake samu a wata ya zarta mafi karancin albashi na Naira dubu 30.

Haka kuma Hukumar ta bayyana cewa laifin da ake zargin Abduljabbar Kabara ba ya cikin laifukan da Hukumar take da hurumin ba wa kariya.

Sai dai wanda ake kara, Abduljabbar Kabara ya ce shi ba ma’aikaci ba ne don haka ba shi da takaimemen albashi.

Har ila yau ya zargi Hukumar da kin yin aiki da abin da addinin Musulunci ya sharadanta cewa, “Duk wanda ya nemi taimako a taimaka masa .

“Haka kuma ko da mutum yana kan ingarmar doki idan ya ce ba shi da wani abu to ya wajaba a ba shi,” inji shi.

Masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Yakubu Abdullahi (PhD) ya roki kotu da ta nemi Gwamnatin Jihar Kano ta Ofishin Kwamishinan Shari’a su bai wa wanda ake kara lauya.

Sai dai Abduljabbar Kabara ya nuna rashin amincewarsa da hakan, inda ya zargi gwamnatin da hada baki da lauyoyin don ganin burinta ya cika.

Ya ce, “Ina da bidiyon da Gwamna Ganduje da kansa yake bayanin cewa ya kai ni mayanka, to yaya zan amince da wanda ya yi waccan magana cewa zai ba ni wanda zai fitar da ni daga mayanka?”

Alkalin Kotun Ibrahim Sarki Yola ya bayyana cewa ya gamsu da dalilan da Hukumar Legal Aid ta bayyana don haka ya sallame su daga shariar.

Haka kuma alkalin ya ce bai gamsu da bukatar masu gabatar da kara ba cewa Kwamishinan Shari’a ya ba wanda ake kara lauya ba.

A cewarsa ba hurumin Kwamishinan Shari’a ba ne hurumin na kotu ne, inda ya kafa hujja da sashe na 349 (5) da na 389 a Dokar Hukunta Laifuffuka ta Jihar Kano (ACJL 2019).

Ya ce kotu tana da damar yin umarni ga wani lauya da ke zaman kansa wanda kuma ke zaune a hurumin kotun da ya tsaya wa wanda ake kara ba tare da ko kwabonsa ba.

Don haka Alkalin kotun ya umarci magatakardar kotun da ya rubuta wa Barista Dalhatu Usman takardar umarnin tsaya wa wanda ake kara.

Daga nan kotun ta dage shariar zuwa ranar 9 ga watan Yuni, 2022.