✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin biliyan N81.5: Pondei ya sume a gaban kwamitin bincike

Ya sume yayin amsa tambayoyi kan zargin facaka da biliyan N81.5 cikin wata biyar.

Mukaddashin Shugaban Hukumar da ke kula da Habbaka Neja Delta (NDDC) Farfesa Kemebradikumo Pondei, ya fadi sume a gaban kwamitin bincike na Majalissar Wakilai.

Pondei a suma ne bayan da fara amsa tambayoyin da Kwamitin binciken ya fara yi masa a ranar Litinin.

An fitar da shi a guje daga cikin dakin taron da ake yi masa tambayoyi a kan facaka da kudaden hukumar.

A makon da ya gabata, Pondei da shugabannin gudanarwar NDDC sun fice daga dakin taron bisa korafin cewa ba za su amince Shugaban Kwamitin na Majalisar ya jagoranci binciken ba.

Ya kafa hujja da cewa Shugaban Kwamitin Majalisar shi kansa akwai zargin rashawa a kansa.

A ranar Litinin din ne kuma Shugaban Kwamitin ya sauka domin bayar da damar shugannin hukumar su kare kansu a gaban Kwamitin.

Kawo yanzu an ce Pondei yana hannun likitocin suna duba lafiyarsa.