✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin damfara: Shari’ar da ake yi wa dan takarar Sanatan APC a Kano ta gamu da tsaiko

Wannan shi ne karo na shida da shari'ar take fuskantar tsaiko

Yunkurin hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na gurfanar da dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar APC, AbdulSalam AbdulKareem Zaura, wanda aka fi sani da A.A Zaura kan zarge-zargen damfara ya sake fuskantar cikas a kotu.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kanon ta dage gurfanar da A.A Zaura don bai wa sabon lauyansa dama ya je ya shirya don tunkarar shari’ar.

EFCC na zarginsa ne da damfarar wani dan kasar Kuwait kudi fiye da Dalar Amurla miliyan daya, zargin da ya sha musantawa.

Duk da kasancewar EFCC ta sami nasarar kawo A.A. Zaura gaban kotun tarayyar amma kotun ta dage zaman shari’ar saboda sabon lauyansa, Basil Hemba bai shirya ba, inda ya ce yana bukatar nazarin yadda zai tunkari batun kasancewarsa sabo kan shari’ar.

Lauyar EFCC Barista Aisha Habib ta nemi kotu ta ci gaba da sauraron shari’ar saboda ta ce sun shirya kuma sun kawo wanda ake zargin kotu, sai dai sabon lauyan A.A. Zaura ya ce bai shirya ba kasancewar sai ranar Lahadi ya karbi kwafin kunshin shari’ar.

Wannan shi ne karo na shida da ake kokarin gurfanar da A. A Zaura, amma har yanzu ba a kai ga karanto masa zarge-zargen da EFCC ke masa a gaban Babbar Kotun Tarayyar ba.

Saboda a cewar Lauyar EFCC Barista Aisha Habib ana ta gabatar da uzuri iri daban-daban.

Daga nan ne Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa ya dage zaman kotun zuwa ranar daya ga watan Maris, don bai wa sabon lauyan damar nazartar kunshin shari’ar.

Aminiya ta rawaito cewa na cewa wata Babbar Kotun Tarayya a 2020 ta sallami A.A. Zaura tare da wanke shi kan duk wani zargi da EFCC ke masa, abin da ya sa EFCC din ta sake gabatar da zargin zamba da ake yi masa tun da farko a kotu.