Zargin kasuwancin kifi a Borno ya tayar da kura a rundunar soji | Aminiya

Zargin kasuwancin kifi a Borno ya tayar da kura a rundunar soji

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai
Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na binciken zargin dakarunta da shiga harkar noma da kasuwancin kifi a yankin Baga da suke yaki da Boko Haram a Jihar Borno.

Kwamitin binciken rundunar ya yi wa Kwamandan Bataliya ta 130 da ke Baga, Laftanar Kanar Umar Abdulmajid da ‘yan civilian JTF tambayoyi kan zargin a garin da ya shahara da kasuwancin kifi.

Zargin Sojojin Rundunar Operation Lafiya Dole mai yakar Boko Haram ya kara karfi ne bayan harin da kungiyar ta kai wa Gwamna Babagana Zulum na Jihar a Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar.

Harin a yankin da a karkashinsa garin Baga wanda ya yi fice da kasuwancin kifi yake ya haifar da kakkausan suka ga sojojin da ke alhakin samar da tsaro a jihar.

Ana zargin cewa ana yi wa sojojin da suka shiga harkokin dako kifi daga Baga zuwa Maiduguri da wasu wurare domin sayarwa.

Mataimakin kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Felix Omoigui ya jagoranci kwamitin binciken da rundunar Sojin ta Kafa domin ziyarar gani da ido a Baga.

Kwamandan Bataliyar ta 130 ya musanta zargin da cewa babu inda sojoji suka shiga kasuwancin kifi ko noma a fadin yankin Tabkin Chadi.

“Babu inda farar hula ballantana sojoji suke noma. Kai daga Monguna har zuwa Baga kaf babu fararen hula kuma babu motocin fararen hula da ke zuwa Baga”, inji shi.

Manjo Janar Felix Omoigui ya shaida wa ‘yan jarida cewa Shugaban Rundunar Laftanar Janar Tukur Buratai ya umarce su ne su je su gano gaskiyar lamarin domin ba zai lamunci karya doka ba.

“Mun yi bincikenmu, wanda tare da ku muka je kuma a fili aka yi komai. Yanzu mun bar ku muku alkalanci

“Za mu rubuta sakamakon binciken wanda idan na kammala za mu mika wa mahukunta rahoton. Idan da bukata za mu yada shi.

“Zargin abun damuwa ne domin yana neman zubar da kimarmu shi ya sa shugaban rundunar soji ya damu ya kuma sa a yi bincike.

“Kun dai ga ko’ina, babu fararen hula kuma babu wata gona da ake nomawa, amma ban san daga ina jita-jitar ta samo asali ba.

“Ba na so in yanke hukunci yanzu saboda ba a kai ga kammala bincike ba, amma zuwa yanzu abun da muka gani ya nuna zargin ba shi da tushe.

“Ba mu dade da ‘yanto wurin nan ba muna samar da tsaro a ciki domin fararen hula su iya dawowa.

“Amma mukan dan samu yunkurin ‘yan tayar da kayar baya na shigo. Abun da ke faruwa ke nan.

“To me zai sa wani soja ya bar babban abun da ya kawo shi na kare fararen hula ya fara noma? Da wuya”, inji Omoigui.