✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin N5.6bn: Buhari ya sallami Shugaban NIRSAL

Sallamar Aliyu Abdulrasheed daga shugabancin NIRSAL ba zai rasa alaka da zargin almundahana a hukumar ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Manajan Daraktan Bankin Rancen Noma (NIRSAL) daga aikinsa.

Ana hasashen sallamar Aliyu Abdulrasheed daga shugabancin NIRSAL ba zai rasa alaka da zargin almundahana a hukumar ba.

A watan Janairu, wani binciken kwakwaf da kafar Daily Trust ta yi ya bankado yadda wasu jami’an Hukumar NIRSAL suka hada baki da wasu kamfanoni uku da bankin ya ba wa rancen noman ranin alkama mai fadin kadada 20,000 a jihohin Kano da Jigawa suka karkatar da kudaden.

Tun a lokacin Aliyu Abdulhameed ya musanta zargin da cewa ba shi da tushe kuma an kitsa ne domin bata sunansa da na hukumar.