✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin safarar sassan jikin mutum: Kotun Birtaniya ta ki ba da belin Ike Ekweramadu

Kotun ta ba da umarnin tsare shi har 7 ga watan Yuli

Kotun majistare da ke birnin Uxbridge a Birtaniya ta ki amincewa ta ba da belin tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweramadu da matarsa, Beatrice, wadanda aka kama bisa zargin cinikin sassan jikin mutum.

Aminiya ta rawaito yadda ’yan sandan birnin Landan suka kama da miji da matar.

Kotun dai ta ki amincewa da bukatar ba da belin, inda ta ba da umarnin ci gaba tsare shi har nan da ranar bakwai ga wata Yuli.

Sashen Kula da Laifuffuka na ’yan sandan birnin ne suka cafke shi tare da matar tasa, Beatrice.

A cewar kafar yada labarai ta Sky News, ana zargin mutanen ne da hada baki don cire wani sashe na jikin wani yaro, amma daga bisani an ceto shi kuma yanzu yana hannun kulawar gwamnati.

Kafar ta rawaito cewa, “Beatrice Nwanneka Ekweramadu mai shekara 55 da Ike Ekweramadu mai shakara 60, yanzu haka an tsare su a kurkuku, kuma za su bayyana a gaban kotun majistare ta Uxbridge a yau [Alhamis].

“An tuuhumi mutum biyun ne, wadanda dukkansu ’yan Najeriya ne, bayan wani bincike da sashen binciken laifuka na ’yan sandan birnin Landan suka gudanar.

“Yanzu dai an ceto yaron.

“An fara binciken ne bayan an ankarar da ’yan sanda kan laifin a ranar 22 ga watan mayun 2022, wanda wani salon bautar da mutane ne na zamani,” inji ’yan sanda.