✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin zagon kasa: Aisha Buhari ta saki bidiyon El-Rufai

Matar Buhari ta saki bidiyon Nasir El-Rufai yana zargin kusoshin gwamnatin Buhari na yi wa takarar Tinubu kafar ungulu.

Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, ta saki wani bidiyon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai yana cewa akwai wasu kusoshin gwamnati na yi wa takarar Bola Tinubu na jam’iyarsu  ta APC kafar ungulu.

Aisha ta wallafa bidiyon ne a shafinta na Instagram ranar Laraba.

Da safiyar ranar ce a wani shirin siyasa na  tashar talabijin ta Channels, El-Rufai ya ce bakin cikin faduwar dan takarar masu kafar ungulun a zaben fidda gwanin APC ne ya sanya suke wa Tinubu zagon kasa.

Gwamnan ya ce akwai wasu kusoshin gwamnatin APC da ke fakewa da aniyar shugaban kasa na yin abin da yake ganin shi ne daidai suna kawo wa takarar Bola Tinubu cikas, amma bai kama sunan kowa ba.

“Suna kokarin su saka mu fadi zabe ta hanyar buya bayan tagiyar shugaban kasa suna mana zagon kasa.

“Misali batun cire tallafin man da ke lashe tiriliyoyin Naira da a baya duka muka amince da shi,” in ji El-Rufai.

Sanya bidiyon da mai dakin shugaban kasar ta yi dai ya janyo mahawara tsakanin ’yan Najeriya a kafofin sada zumunta.