‘Zazzabin cizon sauro na kashe mutum daya duk minti 6 a Najeriya’ | Aminiya

‘Zazzabin cizon sauro na kashe mutum daya duk minti 6 a Najeriya’

    Abubakar Muhammad Usman

Wani binciken shirin dakile cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya ya gano cewa akalla mutum daya ne ke mutuwa sakamakon kamuwa da ciwon duk cikin minti daya a kasar.

Da yake jawabi a ranar zazzabin cizon sauro ta duniya, Kwamishinan Lafiya na Jihar Adamawa, Abdullahi Isa, ya ce mutum 90,000 da suka mutu a Najeriya na da alaka da zazzabin cizon sauro a duk shekara.

Kwamishinan ya yi gargadin cewar cutar na daga cikin manyan cututtukan da suka addabi duniya, musamman ma Afrika.

Ya ce “A baya-bayan nan, binciken shirin dakile cutar zazzabin cizon sauro, ya bayyana yadda mutum 90,000 suka mutu sakamakon cututtukan da ke da alaka da zazzabin cizon sauro a Najeriya.

“Mutum tara cikin 10 na ’yan Najeriya na mutuwa ne a sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro a kowane awa daya,” inji Kwamishinan.

Sai dai ya bayyana yadda aka samu ci gaba inda cutar ta sami koma-baya daga kashi 27 cikin 100 a 2015 zuwa kashi 23 a 2018.

Har wa yau, ya ce za a iya shawo kan kamuwa da cutar ta hanyar bai wa yara ’yan kasa da shekara biyar a duniya kulawa ta musamman.

“Adamawa na bakin kokarinta wajen ba da tallafin da ya dace don yaki da zazzabin cizon sauro,” a cewarsa.