✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa: Mutum 6 sun mutu, 76 sun harbu a Gombe

An gano cutar ne bayan wasu almajirai biyar sun fara rashin lafiya, an kai su asibiti.

Akalla mutum shida ne suka mutu sakamakon harbuwa da cutar zazzabin Lassa, yayin da wasu 76 suka kamu a Karamar Hukumar Kaltungo da ke Jihar Gombe.

Wani jami’i karamar hukumar ya bayyana cewa cutar ta bulla ne a wata makarantar almajirai da ke mazabar Dogon Ruwa, a ranar 11 ga watan Afrilu.

Da take tabbatar da hakan, Shugabar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na Karamar Hukumar Kaltungo, Comfort Danlami, ta ce an gano cutar ne bayan wasu almajirai biyar sun fara rashin lafiya, an garzaya da su asibiti.

“Da farko an yi zargin suna fama da cutar sankarau ne, amma daga bisani bayan an yi musu gwaji sai aka gano suna dauke da zazzabin Lassa.

“An tabbatar da rasuwar biyar daga cikin wadanda suka kamu da cutar, malaminsu kuma ya fara rashin lafiya a ranar Lahadi, daga bisani ya ce ga garinku nan,” a cewarta.

Ta bayyana a ranar Laraba, yayin wata ziyara ga tawagar hukumar bayar da agajin Jihar Gombe (GoHealth), ta kai fadar Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammed.

Shugabar ta kara da cewar tuni kwamitin yaki da cutar ya shirya shiga lungu da sako don wayar da kan jama’ar jihar game da cutar.

Ta ce har wa yau, an kafa cibiyar killace wadanda suka kamu da cutar, kuma kawo yanzu akwai mutum daya a killace a cibiyar yana ci gaba da karbar kulawa.

Kazalika, ta ce an samu mutum 76 da suka harbu da cutar bayan gudanar da gwajin cutar kan wasu mutane da ake zargin suna dauke da cutar.