✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa ya kashe Likita a Zariya

Za a yi gwaji samfurin jinin mamaci a Abuja.

Ana fargabar cewa Zazzabin Lassa ya hallaka wasu mutane biyu yayin da mutum daya a halin yanzu ke gadon jinya a asibiti a Zariya.

Daga cikin mamatan akwai wani likita, Dokta Abubakar Saleh Morike wanda ya ajali ya katse masa hanzari safiyar Litinin a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Wakilinmu ya ruwaito cewa yadda aka gudanar da jana’izar likitan ta jefa shakku a tsakanin al’umma, la’akari da hana kowa ya kai wa kusa da gawarsa da aka yi har aka binne shi.

Tun a ranar Asabar da ta gabata ce daya daga cikin masu taimaka wa likitan a wurin aiki mai suna Hamza, ya riga mu gidan gaskiya sakamakon rashin lafiya mai yanayi da ta uban gidansa.

Haka kuma, wani abokin aikin nasu mai suna Ibrahim yana kwance a asibiti inda ake ci gaba da duba lafiyarsa.

Bayanai sun ce tun a ranar Alhamis aka kai likitan Asibiti Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello a reshensa da ke Tudun Wada, inda daga bisani aka mayar da shi babban reshen asibitin da ke Shika.

Aminiya ta ruwaito cewa, Dokta Moriki yara su ne a daren Lahadi wayewar garin Litinin, kuma an gudanar da jana’izarsa a gidan mahaifinsa da ke Tudun Jukun  a garin na Zariya da misalin karfe 9.00 na safe sannan aka kai shi makabartar Dambo.

Wani babban jami’i a asibitin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa yanzu haka ma an dauki samfurin jinin marigayin domin yin gwajinsa a Abuja, babbar birnin kasar.

A nasa bangaren, Dokta Hamza Ibrahim Ikara, Daraktan Sashin Yaki da Yaduwar Cututtuka na Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko reshen Jihar Kaduna, ya ce za su hada gwiwa da asibitin a kan lamarin.