✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa ya kashe likitan Hukumar Lafiya ta Duniya a Binuwai

Sai dai ana zargin karin wasu mutum biyu ma sun mutu sanadin cutar a Jihar.

Wani likita da ke aiki da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Jihar Binuwai ya rasu sakamakon zazzabin Lassa.

Wakilinmu ya rawaito cewa likitan, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Samuel Tagher Nyitor, ya rasu ne ranar Lahadi, bayan an sallame shi daga Asibitin Kwararru da ke Irrua a Jihar Edo, inda ya yi fama da cutar a can.

Sai dai akwai zargin da ake cewa wasu mutum biyu da wani likitan ya duba, su ma sun mutu a sanadin cutar.

Amma Kwamishinan Lafiya da Harkokin Jama’a na Jihar,  Dokta Joseph Ngbea, ya tabbatar wa manema labarai a Makurdi ranar Litinin cewa Samuel Tagher ne kadai aka kai asibitin na Irrua kuma ya mutu.

Dokta Joseph ya kuma ce akwai wani mutum daya da aka tabbatar ya kamu da cutar wanda yanzu haka yana can a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Binuwai (BSUTH), inda ya ce babu wani abin fargaba a ciki.

Kwamishinan ya kuma shawarci al’ummar Jihar da su kauce wa duk wani abin da zai kawo bera a muhallansu.

Ya kuma ce kamata ya yi duk inda aka fuskanci zazzabi mai tsananin da ya ki jin magani a gaggauta kai rahoto don daukar matakin da ya dace.