Zazzabin Lassa ya kashe mutum 2 a Kaduna | Aminiya

Zazzabin Lassa ya kashe mutum 2 a Kaduna

    Abubakar Muhammad Usman

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum biyu a sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa a ranar Laraba.

Daraktan Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa na Jihar, Dokta Hamza Ibrahim Ikara, ya bayyana wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) cewa namiji daya da mace daya ne suka rasu.

Ikara ya ce an samu rahoton bullar cutar ce kananan kananan hukumomin Kubau da Chikun da na jihar.

Ya ce tuni hukumar ta fara gudanar da bincike don gano mutanen da suka yi mu’amala da su kafin rasuwarsu.

Daraktan ya kara da cewa an tura tawaga ta musamman da za ta rika zaga yankunan jihar don wayar da kan al’umma game da illar cutar.

Ya kuma shawarci jama’ar jihar da su kasance masu kula da tsaftar muhallansu, tare da guje wa cin naman daji.