✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa ya kashe mutum 32 a Najeriya

Mutane 759 suka harbu da cutar a fadin jihohi 26 da kuma Abuja.

Bayanai daga Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya NCDC sun nuna cewa akalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu sakamakon zazzabin Lassa cikin makonni uku.

Hukumar NCDC ta ce ya zuwa ranar Asabar mutane 759 suka harbu da cutar a fadin jihohi 26 da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Hakan dai na zuwa ne a yayin da Hukumar ta bayyana cewa ta kaddamar da cibiyoyi daban-daban a dukkan sassan kasar domin yi wa tufkar hanci.

A shekarar 2019, NCDC ta ce an samu bullar cutar guda 796, yayin da a shekarar 2020, an tabbatar da adadin mutane 1,165 da suka kamu da cutar a yayin da ake tsaka da annobar Coronavirus.

Jihohin da abin ya shafa sun hada da Edo, Ondo, Bauchi, Binuwe, Oyo, Taraba, Ebonyi, Kogi, Kaduna, Katsina, Ebonyi, Filato, Kuros Riba, Borno, Anambra, Bayelsa, Jigawa, Kebbi, Ogun, Kwara, Legas, Delta, Gombe, Nasarawa, Ribas da Enugu sai kuma birnin tarayya Abuja.