✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutum 10 a Edo

Mutum 97 aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar

Kwamishinar Lafiya ta Jihar Edo, Farfesa Obehi Akoria, ta ce mutum 10 sun mutu tun bayan bullar Zazzabin Lassa a jihar.

Da take zantawa da manema a Benin, babban birnin jihar, Akoria ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar ya karu zuwa 97.

Ta ce daga cikin wannan adadi, “Etsako ta Yamma na da 38, Esan ta Yamma 24; Esan Arewa maso Gabas 19;  Esan ta Tsakiya 3.

“Esan ta Kudu maso Gabas 2; Etsako ta Gabas 2; Owan ta Gabas 2; Akoko Edo 2; Ovia ta Arewa maso Gabas 2; Oredo 2; sai kuma Etsako ta Tsakiya 1,” in ji shi.

Ta ce gwamnatin jihar ta dauki ingantattun matakai domin yaki da yaduwar cutar a jihar baki daya.

(NAN)